Gwamnatin tarayya ta amince da warware bashin naira biliyan 758 domin biyan ƴan fansho kuɗaɗen su da suke bi tsawon lokaci tun daga shekara ta 2007.
Darakta janar ta hukumar kula da fansho ta ƙasa, Omolola Oloworaran, ce ta bayyana haka a Yola a yayin taron wayar da kai na kwana biyu kan tsarin fansho na haɗin gwiwa da aka shirya ga ma’aikata da masu ritaya daga yankin Arewa maso Gabas.
Oloworaran, wadda kwamishinan gudanarwa na hukumar, Alhaji Bello Abubakar, ya wakilta, ta ce wannan mataki wani muhimmin abu ne da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka domin kawo sauƙi ga tsoffin ma’aikata da kuma dawo da amincewa ga tsarin fansho.
Ta bayyana cewa taron wayar da kan yana daga cikin ci gaban sauye-sauyen da ake yi domin ƙara fahimtar tsarin ga masu shirin yin ritaya da sauran masu ruwa da tsaki.
Ta ƙara da cewa sauye-sauyen sun haɗa da ƙarin fansho ga tsoffin ma’aikata fiye da dubu 241,000 wanda ke wakiltar kashi 80 cikin 100 na waɗanda ke ƙarƙashin tsarin cire albashi kai tsaye bayan ritaya.
Hukumar ta kuma ce an cire jinkirin samun kudin fansho, inda tun daga watan Yuli 2025, masu ritaya ke samun hakkokinsu nan da nan bayan ritaya.
Haka kuma ana shirin dawo da tsarin biyan kudin sallama ga ma’aikatan gwamnati bisa tanadin sashen 4(4) na dokar gyaran fansho ta 2014.
Shugaban hukumar albashi, kuɗin shiga da albarkatun ma’aikata ta ƙasa, Ekpo Nta, wanda mataimakin darektan albashi Chika Ochor ya wakilta, ya ce wannan taro zai taimaka wajen ƙarfafa fahimta kan amfanin tsarin fansho, wanda ke ba da kariya ta kuɗi ga masu ritaya domin su ci gaba da rayuwa ba tare da dogaro da iyalai ko gwamnati ba.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa hukumar kula da fansho ta ƙasa ta shirya wannan taro tare da hukumar kula da albashi, kuɗin shiga da albarkatun ma’aikata ta ƙasa.
NAN













































