Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da hasken lantarki mai amfani da rana a asibitin AKTH Kano

WhatsApp Image 2025 09 17 at 17.25.18 750x430

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta rana mai ƙarfin megawatt 7 a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), domin cire asibitin daga dogaro da wutar lantarki ta ƙasa tare da tabbatar da samun wuta ba tare da yankewa ba ga ayyukan kiwon lafiya.

Ministan kimiyya da fasaha, Cif Uche Nnaji, ya ce aikin ya samo asali ne daga binciken makamashi da hukumar makamashi ta ƙasa (Energy Commission of Nigeria) ta gudanar, inda aka gano cewa AKTH tana buƙatar wutar lantarki mai yawa wacce ake cike ta da dizal mai tsada.

Ya bayyana cewa asibitin yana da bukatar wuta mai ƙarfin megawatt 3.5, tare da kashe kimanin naira miliyan 150 duk wata wajen siyan dizal, lamarin da ya zama ba mai dorewa ba.

Don haka, gwamnatin ta fara aikin samar da mini-grid na wuta mai hasken rana mai ƙarfin megawatt 4, sannan daga baya za a kai shi megawatt 7.

Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, wanda ya tabbatar da saka aikin a cikin kasafin kuɗi na shekarar 2025, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya bada umarnin saka kuɗaɗen aikin bayan korafin da shugabannin manyan asibitoci na koyarwa suka gabatar kan tsadar wutar lantarki da dizal.

Ya ce gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 26 don manyan gyare-gyare a AKTH, ciki har da gina cibiyar kula da masu yawan jini, sashin hoton kashi, sashin bada agajin gaggawa, da kuma na’urorin aikin zuciya.

Ya tabbatar da cewa an riga an ɗauki kamfanin da zai kammala aikin a kan lokaci.

Shugaban asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, ya bayyana aikin a matsayin tarihi ga bangaren lafiya a Najeriya, inda ya ce AKTH zai zama asibitin farko da zai dogara ga wutar lantarki ta kansa.

Ya ƙara da cewa hakan zai rage haɗarin rasa marasa lafiya musamman masu bukatar kulawar gaggawa.

Haka kuma ya sanar da sabbin shirye-shiryen jin ƙai da asibitin ya ƙaddamar, ciki har da kula da jarirai kyauta ga marasa galihu, yin aikin haihuwa ta tiyata kyauta ga mata masu ƙaramin ƙarfi, da samar da motar daukar marasa lafiya domin gaggauta kai su asibiti.

Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki bayan kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya yanke wa asibitin wuta bisa bashin naira miliyan 949.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here