Gwamnatin tarayya tana shirin kafa cibiyoyin sinadarin CNG guda 500 a faɗin ƙasa cikin shekaru uku, domin hanzarta sauya tsarin amfani da makamashi zuwa wanda ya fi tsafta da araha, tare da rage dogaro da fetur.
A cikin sanarwar da Daraktan Gudanarwa na Asusun (MDGIF), Oluwole Adama, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan kammala tattaunawar da aka yi tsakanin MDGIF da kamfanin ƙera kayayyakin China, Endurance Group, kan gina manyan cibiyoyin CNG a ƙasa.
Sanarwar ta ce an cimma matsaya kan kafa wata sabuwar hukuma ta musamman da gwamnati wadda za ta tallafa wa gudanar da aikin, tare da haɗin guiwar MDGIF, Bankin kasuwanci da kamfanonin Endurance Group, da Séquor Investment Partners.
A cewarsa, wannan hukuma da za a kafa mai suna Compressed Natural Gas Auto Mobility Infrastructure Company za ta “kafa cibiyoyin cika CNG guda 500; ta gina tsarin samar da LCNG; ta samar da motocin jigilar CNG da LNG masu ɗauke da kayan iskar gas da za su yi kama da bututun gas a duk faɗin ƙasa.”
Sanarwar ta bayyana cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen hanzarta sauya tsarin amfani da makamashi a Najeriya ta hanyar cike gibi a harkar samar da CNG a ƙasar, tare da faɗaɗa wuraren cika CNG da inganta hanyoyin jigilar iskar domin samun wadatar kayayyaki ba tare da tangarda ba.
Haka kuma ce shirin zai taimaka wajen kawar da dogayen layukan da ake gani a cibiyoyin CNG na yanzu ta hanyar ƙara yawan wuraren cika iskar da sauƙaƙe jigilar kayayyaki.
Matakin ya zo ne yayin da gwamnatin yanzu ke ƙara mayar da hankali kan iskar gas a matsayin madadin mai, musamman bayan cire tallafin fetur da sassauta dokokin kasuwar mai a ƙasa.
Masu ruwa da tsaki a gwamnati sun sha bayyana cewa amfani da motocin CNG zai taimaka wajen rage tsadar sufuri, ƙara tabbatar da tsaron makamashi, da kuma rage matsin lambar da ake yi wa kudaden ƙasashen waje wajen shigo da man fetur.
Najeriya na da fiye da trillion cubic feet 200 na iskar gas, amma ta daɗe tana fama da ƙarancin tsarin samar da iskar a matakin tsakiya, lamarin da ya bar wasu yankuna ba su da wadatacciyar iskar gas.
Shugaban kamfanin Endurance Group, Eric Lin, ya bayyana cewa wannan sabuwar hukuma za ta tabbatar da samar da muhalli mai ɗorewa na wuraren cika CNG da aikin gyare-gyare, tare da kafa tsarin jigila da zai tabbatar da isar da iskar gas ta hanyar madadin bututun gas.
Ya ƙara da cewa tsarin rarrabawa zai ba da damar kai iskar daga manyan cibiyoyin zuwa yankunan arewa da ba su da iskar gas, da kuma wuraren da ake da yawan buƙata a kudu, ta hanyar amfani da cibiyoyi da ake da su da kuma sabon tsarin da ake shirin gina wa.
Ana sa ran cewa kammala wannan shiri zai ƙara yawan amfanin motocin da ke amfani da iskar gas, rage dogaro da man fetur da ake shigo da shi, tare da ƙarfafa yunkurin Najeriya na sauya tsarin makamashin ƙasa zuwa wanda ya fi tsafta.













































