Gwamnatin tarayya na shirin ƙakaba wa wasu jami’o’i Takunkumi

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin tarayya ta sanar da aniyarta ta kakaba takunkumi mai tsauri kan duk wasu jami’o’i da suka kara cibiyoyin karatu ba tare da sahalewar gwamnatin tarayya ba a fadin kasar nan.

Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, inda ya yi gargadin cewa, duk wata cibiya irin wanann da aka kafa ba tare da izinin hukumar kula da jami’o’i ta kasa ko hukumar Ilimin Fasaha da Kwalejojin Ilimi ta kasa ba, za su fuskanci takunkumi.

Ministan ya nuna matukar damuwarsa kan yadda jami’o’in gwamnatin tarayya, da kwalejin fasaha da kwalejojin ilimi ke ci gaba da yin aiki ba bisa ka’ida ba da kuma hujjar kafa cibiyoyin ba.

“Yawancin wadannan sabbin cibiyoyin da ake kirkira ba su da ingantaccen tsarin ilimi, da dabaru da isassun kayan more rayuwa don tabbatar da wanzuwarsu,” in ji shi.

Alausa ya jaddada cewa ba a yarda da yaduwar irin wadannan cibiyoyi ba don kuwa suna lalata martaba da inganci da dorewar tsarin ilimin manyan makarantun Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here