Gwamnatin Najeriya za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 28,000 aiki saboda janye tallafin USAID

91c8522f b775 41ec 9e16 c56250fa7e6b.jpg

Ministan Lafiya na kasa Ali Pate ya ce gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara aiki da mutane dubu 28,000, waɗanda a baya ke aiki da hukumar ba da agaji ta Amurka United States Agency for International Development (USAID).

Da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels ranar Juma’a, ministan ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar gyara ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar yayin da Amurkar ke janye tallafin da take bayarwa ta hannun USAID.

Bayan hawansa mulki ne Shugaban Amurka Donald Truymp ya umarci a dakatar da bayar da tallafi wajen samar da magunguna da ayyuka kamar na cutar HIV a ƙasashe masu tasowa har sai an kammala bincike kan lamarin.

Karanta: Dole ne a binciki zargin da aka yiwa USAID na tallafa wa Boko Haram – Ndume ga Gwamnatin tarayya

Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ba ta zuba kuɗaɗe masu yawa ba a ɓangaren lafiyar, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu “a shirye yake wajen sauya alƙiblar tsarin”.

Ya ƙara da cewa fiye da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeirya daga waje ake shiga da su ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here