Gwamnatin tarayya ta bai wa masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba kwana 30 su dakatar da ayyukansu

0
Illegal Miner

Gwamnatin Najeriya ta bai wa masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba kwana 30, su dakatar da ayyukansu a faɗin ƙasar.

Ministan ma’adinan ƙasar Dele Alake ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar a Abuja.

Alake ya ce duk yunƙurin da gwamnati ke yi wajen mayar da masu haƙar ma’adinan da ba su da lasisi zuwa halastattu ya ci-tura.

Ya ƙara da cewa ma’aikatarsa za ta sake nazarin lasisin masu haƙar ma’adinai a ƙasar a wani ɓangare na sauye-sauyen da yake yunƙurin yi a ma’aikatar.

Ministan ya ce daga cikin sauye-sauyen da yake shirin yi wa ma’aikatar har da ɓullo da kamfanin ma’ainai na ƙasa, da zai haɗa hannu da kamfanonin ma’adinai na duniya, da kuma samar da ‘yan sandan da za su riƙa lura da harkar ma’adinai, tare da samar da bayanan alƙaluman ma’adinai a ƙasar.

A makon da ya gabata ne Ministan ya alƙawarta tsabtace ɓangaren haƙar ma’adinai ta hanyar gabatar da wasu tsare-tsare da ya kira ”masu tsauri” domin daidaita ɓangaren.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here