Gwamnatin Kwara za ta samar da motoci don taimaka wa ɗalibai da ma’aikata

0

Gwamnan jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya AbdulRahman AbdulRazaqAbdulRahman AbdulRazaq ya amince da samar da manyan motoci domin taimakawa wajen jigilar ɗaliban manyan makaratun jihar da ma’aikatan gwamnnatin a birnin Ilorin da kewaye.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Rafiu Ajakaye ya sanya wa hannu, aka kuma wallafa a shafin gwamnatin jihar na Facebook, ta ce an samar da manyan motocin ne domin taimaka wa dalibai wajen rage musu raɗadin da cire tallafin man fetur ya haifar.

Matakin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin rage wa al’ummar jihar raɗadin cire tallafin man fetur, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta ce ”daga ranar Laraba 14 ga watan Yunin da muke ciki za a samar da manyan motoci da za su riƙa jigilar ɗaliba manyan makarantun gaba da sakandire a birnin Ilorin da kewayensa, ciki har da masu zuwa jami’a jiha da ke Malete”.

”Gwamnatin jiha za ta ci gaba da samar da tallafi ga al’ummar jihar Kwara, yayin da najeriya ke tunkarar rayuwa ba tare da tallafin mai ba”, in ji sanarwar.

Tun da farko da gwamnatin jihar ta rage kwanakin aikin gwamnati zuwa wuni uku a faɗi jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here