
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya ƙaddamar da shirin bai wa masu ƙananan sana’o’i wanda zai lashe kuɗi naira biliyan biyar.
Shirin zai samar da kuɗi ga masu ƙananan sana’o’i da kuma tallafa musu a harkar kasuwanci.
Karin labari: Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta dage sauraron hukunci zuwa 13 ga wata
Lokacin da ya ƙaddamar da shirin a garin Katsina, Gwamna Radda ya jaddada cewa ƙananan san’o’i ne ƙashin bayan tattalin arziƙi.
Ya kuma bayyana cewa haɓaka ƙananan san’o’i zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.