Gwamnatin jihar Kano ta amince da shirin yin hadin gwiwa da kamfanin Aqua Power da zai rika sarrafa shara zuwa dukiya da samar da makamashi don dorewar muhalli.
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dr. Dahir M. Hashim ya fitar ranar Juma’a, biyo bayan gabatar da kamfanin.
SolaceBase ta ruwaito cewa Dr. Hashim ya ba da tabbacin cewa kamfanin Aqua Power zai taimakawa kudurin ma’aikatar na yin aiki kafada da kafada don tabbatar da aikin, tare da kokarin sarrafa sharar gida zuwa albarkatu masu mahimmanci da inganta dorewar muhalli, da samar da tattalin arziki.
Ya kuma yi kira ga sauran abokan hulda da masu ruwa da tsaki da su hada kai da kokarin ganin Kano ta zama abin koyi na dorewar shugabanci da muhalli.