Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da wasu mutane da kamfanoni a gaban babbar kotun jihar Kano, domin karɓar kaso na hannu jarinta na kashi 20 cikin 100 a tashar Tsandauri ta Dala da kuma dawo da kuɗaɗen da ake zargin an karkatar kimanin ₦4,492,387,013.76.
A cikin jerin waɗanda ake tuhuma akwai Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar; Abubakar Sahabo Bawuro, tsohon mai ba gwamna shawara ta musamman; Hassan Bello, tsohon babban sakataren hukumar kula da masu jigilar kayayyaki ta ƙasa da ‘ya’yan Ganduje da suka hada da Umar Abdullahi Umar da Muhammad Abdullahi Umar; lauya Adamu Aliyu Sanda; da kuma tashar Tsandauri ta Dala.
Gwamnatin jihar ta zargi waɗannan mutane da aikata laifuka goma, ciki har da haɗin baki wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati, cin amanar jama’a, da yin amfani da mukamai don amfanin kai, wanda ya sa suka karya ƙa’idojin kuɗi da na kundin tsarin mulki.
A cikin takardar tuhumar, an ce waɗanda ake tuhumar sun haɗa kai wajen canja kashi 80 cikin 100 na hannun jari na tashar Tsandauri ta Dala ciki har da na gwamnatin Kano, zuwa wasu kamfanonin sirri da aka ƙirƙira da sunan City Green Enterprise, domin ɓoye asalin mallakar kamfanin.
Haka kuma, an bayyana cewa sun karkatar da sama da ₦4.49 biliyan daga kuɗaɗen gwamnati domin gina hanyoyi, samar da lantarki, da katanga a wajen Dala alhali amfanin kansu da na iyalansu suke nema da hakan.
Gwamnatin Kano ta ce za ta gabatar da shaidu masu ƙarfi, ciki har da jami’in bincike da ya gano ma’amalolin da ake zargi, da wani tsohon abokin haɗin gwiwa a aikin wanda ya shaida yadda aka ƙwace hannun jarinsa.
Shaidar ta kuma nuna cewa wasu takardu na bogi da wasiku na ƙarya aka ƙirƙira domin ruɗar hukumomin da abin ya shafa.
Hujjojin za su nuna cewa an yi amfani da kamfanin Safari Textile Ltd (STL Enterprise) wajen karkatar da Naira Miliyan 750 daga kuɗaɗen jihar Kano, tare da nuna yadda aka bai wa wasu wakilai na ƙarya hannun jari a kamfanin.
Bisa ga bayanan kotu, an mika ƙarar zuwa Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 2, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Yusuf Ubale, amma ba a ƙayyade ranar zaman farko ba tukuna.
NAN













































