Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba tsarin haɗin gwiwa tsakanin ta da ƴan kasuwa domin jawo zuba hannun jari

WhatsApp Image 2025 10 14 at 08.43.22 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin sake nazarin takardun tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP) da ake amfani da su a yanzu.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan mataki na cikin alkawarin gwamnatin yanzu na jan hankalin masu zuba jari nagari da kuma ƙarfafa samun kuɗaɗen masu zaman kansu don hanzarta ci gaban ayyukan raya ƙasa da albarkatun da ba a yi amfani da su ba a jihar.

Shugaban kwamitin sake duba takardun PPP, Alhaji Usman Bala Muhammad, wanda kuma shi ne mai ba wa gwamna shawara kan harkokin jihar, ya bayyana hakan a wajen bude taron bita na kwana uku kan tsarin da aka gudanar a Zariya, Jihar Kaduna.

Ya ce sabbin takardun da aka sake tsara su tare da ƙwararrun masu ba da shawara za su taimaka wajen gina amincewa tsakanin jama’a da masu zuba jari ta hanyar tabbatar da gaskiya da gasa mai kyau a duk wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa.

Ya kuma ce an dauki matakin ne domin magance matsalolin da suka biyo baya daga yarjejeniyoyin da suka gabata da kuma tabbatar da tsarin da zai amfani kowane ɓangare.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar Kano (KanInvest), Aminu G. Sanbauna, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa shugaban kwamitin ya bukaci mahalarta taron su yi aiki tukuru wajen taimakawa samar da takarda mai muhimmanci da za ta haifar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ga al’ummar Kano.

Daraktan hukumar, Muhammad Nazir Halliru, ya bayyana haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu a matsayin wata hanya mafi inganci ta samar da kuɗaɗen maye gurbin tallafin gwamnati wajen gina ayyukan raya ƙasa.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati tana da niyyar samar da tsarin da zai dace da ƙa’idojin duniya kuma ya dore na dogon lokaci.

Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati a majalisar dokokin Kano, Hon. Salisu Kabo Muhammad, ya bayyana goyon bayan majalisar ga wannan shiri na gwamnatin jihar domin gina tsarin da zai bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa ta hanyar amfani da albarkatun jihar yadda ya kamata.

Wakilin ƙungiyar Haɗin gwiwar gudanarwa da kare Muhalli (PACE), Malam Auwalu Hamza, ya nuna tabbacin cewa taron bitar zai samar da ingantaccen tsarin da zai kawo sauyi a harkar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu a Kano.

Babban mai ba da shawara a aikin, Nufi Barnabas, ya yaba da jajircewar gwamnatin Kano, tare da tabbatar da cewa ƙungiyarsa ta yi aiki tuƙuru don samar da cikakken tsarin da ya dace da ƙa’idojin duniya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here