Gwamnatin Kano ta gina rijiyoyin burtsatse mai amfani da hasken rana a manyan asibitoci domin magance ƙarancin Ruwa

WhatsApp Image 2025 12 12 at 09.48.19 750x430

Gwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano Dr Dahiru Muhammad Hashim ya bayyana gagarumin ci gaba da gwamnatin jihar ta samu wajen shawo kan ƙarancin ruwa da ya dade yana addabar manyan cibiyoyin kula da lafiya na jihar Kano.

A cikin sanarwar da ya sanya wa hannu kuma aka aikowa jaridar Solacebase a ranar Alhamis, ya bayyana cewa aikin na daga cikin shirin inganta samun tsaftataccen ruwa a muhimman asibitoci domin tabbatar da ingantacciyar kula da lafiyar jama’a.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Dr Hashim wanda ke jagorantar ayyuka na muhalli da sauyin yanayi ya ce wannan mataki na bin umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf ne domin tabbatar da tsaron ruwa a asibitocin gwamnati.

Ya bayyana cewa asibitoci na daga cikin wuraren da sauyin yanayi ya fi shafar su ta fuskar matsalar ruwa wanda hakan ke da tasiri a bangaren tsafta, tsabtar jiki da ingancin ayyukan kiwon lafiya baki ɗaya.

Karanta: Kano: Hukumar kula da gidajen yari da REMASAB sun ƙulla haɗin gwiwa don inganta tsaftar cibiyoyin gyaran hali

Ya ce gwamnatin jihar ta fara gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a muhimman asibitoci domin ƙarfafa wadatar ruwa da kuma inganta yanayin kula da marasa lafiya.

Sanarwar ta nuna cewa kwamishinan ya duba aikin da ake gudanarwa a asibitin Sheikh Muhammad Jiddah, hukumar kula da asibitocin jihar Kano, asibitin Sir Muhammadu Sunusi, asibitin Gezawa da asibitin Minjibir domin tabbatar da ingancin aiki da bin ƙa’idojin ma’aikata.

Sanarwar ta bayyana cewa an gwada ingancin ruwan rijiyoyin a dakin binciken gurɓataccen ruwa na jihar Kano kuma binciken ya tabbatar da cewa ruwan ya cika ƙa’idar da ta dace da sha.

Sanarwar ta ƙara jan hankalin asibitocin da suka amfana su riƙa kula da kayayyakin yadda ya kamata tare da kira ga masu haƙa rijiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati su rungumi gwajin ingancin ruwa domin kare lafiyar jama’a a fadin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here