Gwamnatin Kano ta dakatar da ƴanjarida 14 daga aiki a gidan gwamnati

Abba Kabir Yusuf 595x430

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da ƴan-jarida 14 da ke aiki a fadar gwamnatin jihar daga aiki tare da neman sauyinsu daga hukumomin da suke ƙarƙashinsu.

A wani saƙo da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga waɗanda abin ya shafa, ya umarce su da su koma wuraren aikinsu, tare da neman hukumominsu su aika da wasu da za su maye gurbinsu a gidan gwamnatin jihar.

Babu wani dalili da kakakin ya bayyana na ɗaukar wannan mataki, illa dai ya buƙace su da su bi umarnin wanda ya fara aiki daga yau Talata.

To amma a saƙon da ya rubuta a shafin WhatsApp na tawagar ‘yanjaridar da ke aiki a fadar gwamnatin jihar ta Kano, Sanusin ya bayyana cewa : ”Abin takaici a lokacin da na yi tafiya zuwa ƙasar Serbia a makon da ya gabata, wasu abubuwa sun faru, saboda haka akwai buƙatar shugabancin a wannan mawuyacin hali ya ɗauki mataki…”

Wasu daga cikin ƴanjaridar da abin ya shafa sun haɗa da na kafofin yaɗa labarai na gwamnatin jihar da na tarayya da kuma masu zaman kansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here