Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya jihar diyya kan dimbin asarar kudade da jihar ta tafka sakamakon hana bukukuwan Sallah.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Alhaji Tajuddeen Usman ne ya yi wannan roko a yau Lahadi da ta gabata a lokacin da mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya kai gaisuwar Sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati.
Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a wajen taron.
Kwamishina Usman ya koka da yadda dokar hana gudanar da bikin hawan Dawakai na gargajiya da aka saba kuma aka hana a yanzu ya sa jihar ta yi asarar miliyoyin Naira na kudaden shiga da za ta iya samu a lokacin bukukuwan Sallah.
Ya kara da cewa, Kano ta dade tana cin gajiyar tattalin arziki daga kwararowar ’yan yawon bude ido na gida da na kasashen waje da ke zuwa jihar musamman domin ganin gagarumin hawan.
“Otal-otal da gidajen cin abinci da masu sayar da abinci na gida da masu harkokin sufuri da kuma masu kananan masana’antu musamman ma wadanda ke da alaka da al’adu kamar su Kasuwar Kurmi, yawanci suna samun babban ci gaban tattalin arziki daga bukukuwan, musamman fararen fata masu yawon bude ido suna kashe kudi sosai a wannan lokacin, kuma duk wannan ya ɓace.”
A cewar Usman, karancin kudi ya haifar da gagarumin gibi a kasafin kudin jihar.
Don haka ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani ta ba Jihar Kano diyyar kudi domin a taimaka wajen dinke barakar da dokar hana fita ta haifar, wanda ya bayyana ba kawai al’adu ba ne, illa ta fuskar tattalin arziki.
Kwamishinan ya jaddada bukatar kiyaye al’adun Kano da kuma dorewar alfanun tattalin arzikin da yake kawo wa, yayin da ya kuma bukaci goyon bayan gwamnatin tarayya don rage asarar da ake yi.
Bikin na Hawan Dawakai wanda aka saba gudanarwa a lokacin bukukuwan Sallah, ya kunshi maharban dawakai, da mawakan gargajiya, da raye-raye, kuma ya kasance daya daga cikin abubuwan da ke jan hankalin al’ummar Kano da ma duniya baki daya.













































