Gwamnatin Kano ta ayyana ranar Litinin a matsayin hutu bisa rasuwar ƴan wasa

Abba Kabir Yusuf Abba

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matukar alhininsa tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 22 tare da jikkata wasu da dama.

SolaceBase ta ruwaito cewa mutanen da lamarin ya rutsa da su, wadanda galibinsu a shekarun kuruciya suke, suna komawa gida ne a matsayin tawagar Kano daga gasar wasanni ta kasa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

“A madadin gwamnati da na al’ummar jihar Kano, muna mika sakon ta’aziyyarmu kan abin alhinin da ya faru ga gwarazan tawagar Kano a hanyarsu ta dawo wa gida kan hanyar Kano zuwa Zariya,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa tawagar ta kunshi ’yan wasa da masu ba da horo da jami’an da ke wakiltar jihar a wasanni daban-daban a wajen bikin wasannin kasa da aka kammala.

Gwamna Yusuf ya bayyana lamarin a matsayin iftila’in da ba za a manta da shi ba ga daukacin jihar, tare da  yin kira da a kwantar da hankula tare da bayar da hadin kai da addu’o’i.

Ya kuma ba da tabbacin cewa, ana yin duk mai yiwuwa don tallafa wa wadanda abin ya shafa da iyalan su wadanda suka rasu.

Yayin da mai girma gwamna ya tafi kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025, ya bayar da umarnin a ware ranar Litinin 2 ga watan Yuni 2025 a matsayin ranar hutu ga al’ummar Kano da su yi addu’a tare da jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Jihar ta kuma yi kira ga limamai da dukkan musulmin da ke ciki da wajen Kano da su yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da iyalansu ya jikan wannan rashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here