Gwamnatin Kano ta aika ƙorafe-ƙorafe kan Sheikh Lawan Triumph zuwa Majalisar Shura

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta shiga tsakani a muhawarar da ta taso kan kalaman da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Triumph, ya yi a yayin wani darasi, inda ta umarci cewa a mika duk ƙorafe-ƙorafe da na goyon baya da kungiyoyi suka gabatar zuwa ga Majalisar Shura domin ta yi nazari da bayar da shawara.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa al’amuran sun biyo bayan darasin da Sheikh Triumph ya gabatar a ranar 15 ga Satumba, 2025 lokacin da yake bada darasi a cikin littafin Aqidatul Tahawiyyaha a Masallacin Alƙur’ani da ke Bachirawa, inda ya yi watsi da tsoffin labarai da ake yadawa game da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

A cikin hudubarsa, Sheikh Triumph ya kalubalanci ra’ayin cewa Annabi an haife shi da kaciya da kuma ‘yan kwayoyin kwalliya a idanunsa, yana mai cewa irin waɗannan siffofi ba su da na musamman ga Annabi kaɗai domin ma mutane da dabbobi kan kasance da su.

Wannan furuci ne da ya jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar Musulmi a jihar.

Kungiyoyin addini da dama ciki har da Safiyatul Islam ta Najeriya, Kungiyar Matasa masu wayar da kai ta Tijjaniyya, Ƙungiyar Malaman Sunnah, da Iimaman masallatan Juma’a na Qadiriyya, sun aika da ƙorafe-ƙorafe ga gwamnati suna neman a ɗauki mataki a kan malamin.

Sai dai kuma wasu malamai da Dr Abdallah Gadon Kaya ke jagoranta sun bayar da wasikar goyon baya ga Sheikh Triumph, inda suka nemi gwamnati ta kare shi da fahimtarsa.

Mai magana da yawun sakataren gwamnatin jiha, Musa Tanko, ya tabbatar da karɓar ƙorafe-ƙorafen tare da bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a mika su gaba ɗaya ga Majalisar Shura.

Majalisar, wadda ta ƙunshi manyan malamai, za ta yi nazari a kai sannan ta ba gwamnati shawara kan matakin da ya dace.

Sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kasancewa a tsaka-tsaki a wannan lamari, tare da mai da hankali kan tabbatar da zaman lafiya da ɗorewar hadin kai na addini a Kano.

Ya kuma bukaci jama’a su kwantar da hankulansu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum yayin da ake jiran hukuncin Majalisar Shura.

Jihar Kano na daga cikin wuraren da aka fi samun tattaunawar addini mai tsanani a Arewacin Najeriya, inda bambancin fahimtar nassosin Musulunci kan haifar da muhawara, ƙorafe-ƙorafe, da ma zanga-zanga daga kungiyoyi daban-daban.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here