Gwamnatin Kano ta ɗage aikin tsaftar muhalli na ƙarshen wata

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano ta sanar da dakatar da aikin tsaftar muhalli na karshen wata da aka tsara gudanarwa gobe Asabar.

Daraktar wayar da kai ta ma’aikatar, Maryam Abdulkadir, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa an dakatar da aikin ne saboda bikin gargajiya na Kalankuwa a Kano da za a gudanar a wannan rana.

Ya ce wannan biki na daga cikin manyan al’adun jihar da ke nuna tarihin Kano, al’adunta da kuma dabi’un gargajiya na mutanen jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here