Gwamnatin jihar Taraba ta rufe makarantun kwana saboda ƙaruwar matsalolin tsaro

Taraba Governor Kefas 720x430

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya umarci dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu da ke jihar su rufe makarantun kwana nan take domin dakile ƙaruwar matsalolin tsaro.

A cikin wata sanarwa da kwamishiniyar ilimi Dr. Augustina Godwin ta fitar a ranar juma’a, ta bayyana cewa ƙarin barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan ya mayar da ɗaliban kwana cikin haɗarin kamuwa da hare-haren ’yan bindiga, musamman ganin sace-sacen dalibai da aka yi a jihohin Kebbi da Niger kwanan nan.

Sanarwar ta ce gwamnan ya umurci cewa dukkan makarantun sakandare su koma tsarin zuwa daga gida a kullum har zuwa wani lokaci, tare da tabbatar da cewa shugabannin makarantu da masu mallakar su sun aiwatar da umarnin cikin gaggawa.

Karanta: Makarantar Catholic a Neja: Ɗalibai da Makamai 227 aka sace – ƙungiyar kiristocin Najeriya

Ta bayyana cewa wannan mataki na kariya ne da aka ɗauka domin kare ɗalibai da kuma dakile yiwuwar keta tsaro a wannan lokaci da tashin hankali ke ƙaruwa a yankin.

Godwin ta tabbatar wa iyaye cewa gwamnatin jihar na aiki tare da jami’an tsaro domin dawo da kwanciyar hankali tare da inganta matakan kare rayuka a makarantun jihar.

Ta kuma ce an bukaci shugabannin makarantu da su tabbatar da bin umarnin gaba ɗaya da kuma ƙara sa ido a cikin harabar makarantunsu.

Lamarin na zuwa ne bayan da wasu daliban makarantar St. Mary’s da ke Papiri a jihar Niger aka sace su a daren juma’a, wanda ya biyo bayan wani harin da aka kai a Maga, jihar Kebbi inda aka sace dalibai mata 25 a makon da ya gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here