Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 41 da zai duba shawarwarin samar da sabbin masarautu da gundumomi a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar ga manema labarai a Bauchi yau Litinin.
A cewar sanarwar, kwamitin ya kunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo su daga bangarori daban-daban, da suka hada da sarakunan gargajiya da masu fasaha da malamai sai wakilan kungiyoyin fararen hula da ma’aikatan shari’a da hukumomin tsaro da kuma kungiyoyin addini.
“Wannan shiri ya biyo bayan kiran farko da gwamnatin jihar ta yi na gayyatar al’umma don gabatar da bukatunsu na kirkiro sabbin masarautu da gudumomi.
“An dora wa Kwamitin alhakin tantance abubuwan da aka gabatar bisa ga daidaito da hada kai da siyasa da dorewar kudaden gwamnati.
“Gwamna Mohammed zai kaddamar da kwamitin a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuli a zauren majalisar zartaswa na gidan gwamnati da ke birnin Bauchi da karfe 10:00 na safe,” in ji Gidado.
Gidado ya ce, an gudanar da tsarin ne domin karfafa cibiyoyin gargajiya, da inganta harkokin cikin gida wajen gudanar da harkokin mulki da kuma kiyaye al’adun gargajiya na jihar.












































