Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita tsawon sa’o’i 24 a ƙaramar hukumar Lamurde

Rabiu Kwankwaso 2 750x430

Gwamnatin jihar Adamawa ta kafa dokar hana fita a tsawon sa’o’i 24 a yankin ƙaramar hukumar Lamurde, nan take ba tare da wani jinkiri ba.

Wannan umarni ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Hussaini Hammangabdo, ya fitar a ranar Litinin, inda aka bayyana cewa matakin ya biyo bayan sake barkewar rikicin ƙabilanci da ya ɓullo a daren Lahadi a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa wasu dakarun ƙabilar Chobo masu makamai daga makwabciyar jihar Gombe sun haɗu da takwarorinsu na jihar Adamawa, inda suka kaddamar da hare-hare cikin tsari a kan al’ummomin Bachama da ke cikin ƙaramar hukumar Lamurde, lamarin da ake tsoron ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Wadansu majiyoyi daga yankin sun ce maharan sun taso daga rafukan da ke iyaka da Gombe, inda suka mamaye wasu al’ummomi daga gabas zuwa yamma, tare da fatattakar mutanen garuruwan Tingno, Waduku da wasu ƙauyuka biyu.

Hammangabdo ya bayyana cewa an riga an umurci hukumomin tsaro da su gaggauta dawo da doka da oda a yankin, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnatin jihar ta kuma roƙi mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bin ka’idojin tsaro, domin kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a Lamurde.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here