Gwamnati za ta ƙara yawan mutanen da za ta baiwa tallafin kuɗi

Gwamnati, Tinubu, musanta, kudi, kasafi
Fadar shugaban Najeriya ta musanta zargin yin coge a kasafin kudin 2024 wanda Shugaban kasar ya sanyawa hannu a watan Janairu. Ɓangaren zartarwar ta mayar...

Gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Bola Tinubu na shirin sake fara baiwa talakawan kasar da kuma mafiya rauni miliyan 12 kuɗaɗen tallafi.

A halin yanzu, kusan mutane miliyan uku ne ke amfana da wadannan shirye-shiryen na tallafi, amma saboda tsadar rayuwa, gwamnati na sa ran karin iyalai miliyan 12 za su cancanci karɓan wadannan kudade.

Ministan kudi da tattalin arziki Wale Edun ne ya sanar da wannan shirin yayin wani taron ma’aikata a Uyo, da ke jihar Akwa-Ibom.

Karin labari: Cutar lassa ta kashe mutane 4 a asibitin soji da ke Kaduna

Ministan ya ce manufar ita ce a bayar da tallafin kuɗi ga al’ummar da ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki domin magance buƙatunsu na gaggawa, ta yadda za’a rage talauci.

Shawarar sanar da shugaba Tinubu kan shawarar kwamitin ɗin kafin a kammala rahoton karshe shi ne a sanar da shi abubuwan da ke faruwa.

Edun ya jaddada yin amfani da fasaha don tabbatar da biyan kuɗi mai inganci da gaskiya, da guje wa ayyukan hannu da jinkiri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here