Gwamnan Kebbi ta dakatar da babban sakatare saboda alaƙanta jihar da yawan ‘yan luwadi da madigo

Nasir Idris 2 750x430

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da babban sakatare na majalisarsa Nasiru Abubakar Kigo, saboda ikirarin cewa jihohin Kebbi da Sokoto ne suka fi yawan ‘yan luwadi da madigo.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan Ahmed Idris, ya tabbatar da dakatarwar har zuwa wani lokaci a ranar Juma’a.

A cewarsa, an ba da takardar dakatar da babban sakataren daga shugaban ma’aikata na jihar Kebbi, Malami Shekare, wadda ke cewa: “A bisa ka’idar aikin gwamnati za ku ci gaba da zama a dakace har sai an kammala bincike kan ikirarin ku na yawan ‘yan luwadi da madigo a jihar Kebbi, bayanin da kuka yi ya kunshi rashin da’a a tsakanin al’umma.

Kwanan nan, gwamnatin jihar Kebbi, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta karyata ikirarin Kigo, inda ta bayyana shi a matsayin zance maras tushe.

Kigo wanda shi ma malamin addinin Islama ne ya yi wannan tsokaci mai cike da ce-ce-ku-ce a watan Ramadan a wani taron karawa juna sani da aka gudanar a Estate Adamu Aliero da ke Birnin Kebbi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here