Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabbin naɗe-naɗe a muƙamai daban-daban tare da ƙarin girma ga wasu jami’ai a aikin gwamnati.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Abubakar Ibrahim Matawalle, wanda aka naɗa a matsayin shugaban na rikon ƙwarya na hukumar kula da jin daɗin alhazan jihar Kano, yayin da aka ƙara wa Yusuf Mukhtar girma zuwa matsayin babban sakatare na dindindin.
Sauran sun haɗa da Barrista Rahama Malam Alhaji, wadda aka naɗa a matsayin shugabar kwalejin yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, da kuma Aina’u Ade wadda aka ƙara mata girma daga mataimakiya ta musamman zuwa babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin Kannywood.
Sanarwar naɗe-naɗen na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa Abubakar Ibrahim Matawalle ya taɓa riƙe muƙamin sakataren zartarwa na hukumar jin daɗin alhazan jihar Kano da kuma babban sakatare a ma’aikatar tsare-tsare kafin ya yi ritaya daga aikin gwamnati a jihar Kano, inda ya fara aiki daga matsayin mataimakin sakatare har ya kai babban sakatare, sannan ya yi ritaya a 2014 bayan ya shafe shekaru 8 a wannan matsayi.
Rahama Malam Alhaji ƙwararriyar lauya ce mai gogewa fiye da shekaru 7 a fannonin shari’ar kotu, shari’ar kamfanoni, dokokin lantarki, bin ƙa’idojin hukuma da sasanta rikice-rikice, inda ta yi aiki a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano da kuma fannin ilimi a matsayin shugabar makarantar koyar da lauya ta jami’ar Maryam Abacha ta Amurka da ke Najeriya.
Ƙarin girma da aka bai wa fitacciyar jarumar fim Aina’u Ade daga mataimakiya ta musamman zuwa babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin Kannywood ya biyo bayan rawar gani da ta taka a tsohon muƙaminta, inda gwamnan ya sanar cewa dukkan naɗe-naɗen da ƙarin girman sun fara aiki nan take, tare da buƙatar waɗanda aka naɗa su yi aiki tuƙuru, su kasance masu gaskiya da biyayya ga ajandar Kano First.













































