Gwamnan Kano ya yi ƙarin bayani kan wanda zai ci gaba da kasancewa Sarki a jihar 

WhatsApp Image 2026 01 17 at 01.27.38 750x430 (1)

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi karin haske kan rikicin masarautar Kano da ya dade yana gudana, bayan jita-jitar da ta sake tasowa game da yiwuwar sauyin matsayi na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, sakamakon sabon tsarin siyasar da gwamnan ya shiga da gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya bayyana cewa sabon matsayarsa ta siyasa ba zai shafi matsayin Sarkin Kano ba, yana mai cewa Muhammadu Sanusi na biyu na nan daram a matsayin Sarkin Kano, kuma babu wani shiri ko mataki da gwamnatin jiharsa ke dauka na sauya wannan matsayi.

Tsawon kusan shekaru biyu, Jihar Kano ta fada cikin rikicin sarauta da ba a taba ganin irinsa ba, inda sarakuna biyu ke ikirarin kasancewar su Sarkin Kano.

Muhammadu Sanusi na biyu ya ci gaba da zama a fadar Gidan Rumfa, yayin da Aminu Ado Bayero ke zaune a karamar fadar Nassarawa, kowanne na samun goyon bayan bangarorin siyasa daban-daban.

An sauke Muhammadu Sanusi daga karagar mulki a watan Maris na shekarar 2020 a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, inda aka nada Aminu Ado Bayero a madadinsa.

Sai dai a watan Mayun shekarar 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sanusi kan karagar mulki.

Mayar da Sanusi kan sarauta ya biyo bayan amincewar Majalisar Dokokin Jihar Kano da dokar soke dokar majalisun masarautu ta shekarar 2019, wadda ta kafa masarautu biyar a jihar, dokar da ake ganin ita ce ta haifar da sauke Sanusi daga sarauta tun farko.

Da soke wannan doka, gwamnatin Yusuf ta dawo da tsarin masarauta guda daya a Kano, inda ta cire Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan da aka nada a karkashin tsarin da ya gabata.

Duk da haka, Aminu Ado Bayero ya ci gaba da ikirarin cewa shi ne Sarkin Kano, inda rahotanni ke nuna yana samun kariyar tsaro da kuma amincewa a fakaice daga wasu bangarorin gwamnatin tarayya, lamarin da ya kara tsananta rikicin.

Rikicin ya jawo rabuwar kawuna a cikin masarautar Kano, tare da raba ra’ayi a cikin gidan sarauta da al’ummar jihar, yayin da siyasa ke kara yin tasiri a harkokin gargajiya.

Rikicin ya sake daukar sabon salo ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a farkon wannan makon, lamarin da ya hada shi da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake dauka a matsayin babban mai goyon bayan Aminu Ado Bayero.

Sauya shekar ta kuma haifar da tsaiko a alakar Yusuf da tsohon mai daukar nauyinsa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a karkashinsa ake ganin Muhammadu Sanusi ya samu damar komawa kan sarauta.

Wannan sauyin siyasa ya haifar da jita-jitar cewa za a iya sake duba rikicin masarautar a matsayin wani bangare na sasanta rikicin cikin jam’iyyar APC.

Jita-jitar ta kara karfi ne bayan Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya nuna alamun cewa rikicin na iya kusantowa karshe, inda ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakai na zahiri domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Waiya ya nuna cewa rikicin sarakunan biyu na dab da warwarewa, abin da ya sa wasu ke ganin akwai yiwuwar cimma matsaya ta siyasa, ko dai ta hanyar dawo da Aminu Ado Bayero da cire Sanusi, ko kuma barin Sanusi tare da bai wa Bayero wata dama ta siyasa a matakin tarayya.

Jita-jitar ta yadu sosai a kafafen sada zumunta, inda wasu ke alakanta ta da sabuwar sabani tsakanin Gwamna Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta duk wani shiri na cire Muhammadu Sanusi daga sarautar Kano, yana mai jaddada cewa nadin sarkin ya kasance ne bisa doka bayan soke dokar masarautu, kuma babu wani shiri na yin gyara ko sauyi a wannan mataki.

Ya bayyana cewa sauya shekarsa zuwa APC ba za ta sauya halin da ake ciki ba, domin Muhammadu Sanusi shi ne Sarkin Kano kuma babu wani shiri ko niyya na sauya shi.

Gwamnan ya bayyana jita-jitar a matsayin rade-radi marasa tushe daga wasu da ba sa fatan alheri ga Jihar Kano, yana mai kira ga al’umma da su yi watsi da irin wadannan labarai.

Ya kuma jaddada cewa masarautar gargajiya ba ta cikin tsarin siyasa, yana mai cewa matakin da gwamnatinsa ta dauka shi ne domin dawo da mutunci da kima ga wannan tsari na gargajiya.

Game da yiwuwar tuntubar bangaren Aminu Ado Bayero, gwamnatin jihar ta bayyana cewa har yanzu ba a fara irin wannan tuntuba ba, sai dai ana kira ga bangaren da ya jawo rikicin da su fifita zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban jihar.

Haka kuma gwamnatin ta bukaci Aminu Ado Bayero da ya nisanci ba da damar amfani da shi a harkokin siyasa, tare da bada gudunmawa wajen tabbatar da tsaro da ci gaban Kano.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a shirye take ta tattauna da duk wanda ke da ra’ayin da zai taimaka wa ci gaban Kano, domin cewa muradun Kano sun fi kowanne mutum ko siyasa muhimmanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here