Gwamnatin jihar Kano ta raba sama da Naira miliyan 642 a matsayin diyya ga sama da mutane 200 da ibtila’in zaizayar ƙasa ya shafa a kauyukan Bulbula-Gayawa a kananan hukumomin Ungoggo da Nasarawa.
Duk da cewa bankin duniya ne ke tallafawa shirin da Shirin bunkasa aikin Noma da Dakile Matsalar kamfar Ruwa a wuraren Tsandauri wato ACRESAL na yaki da zaizayar kasa a yankin da Naira biliyan 8.4.
SolaceBase ta bayar da rahoton cewa, gabatar da tallafin wanda ya gudana a ranar Alhamis, ya nuna wani babban mataki a kudurin jihar na sake farfado da muhalli da kuma taimakon jin kai ga wadanda suka rasa matsugunansu ko kuma tabarbarewar tattalin arziki.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda shi da kan sa ya sa ido a kan rabon kudin ya bayyana cewa, matakin na cika alkawari ne da kuma tabbatar da adalci ga al’umma.
“Na yi matukar farin ciki da zuwa nan da kaina na gabatar da takardar biyan diyya ga mutanen da abin ya shafa a karkashin shirin sake tsugunar da wadanda aikin kawar da zaizayar Bulbula-Gayawa ya shafa a kananan hukumomin Nasarawa da Ungogo.”
Ya ci gaba da cewa, “Kudaden da muke rabawa a yau Naira miliyan dari shida da arba’in da biyu (N642,000,000) muna fatan za ku yi amfani da wannan kudi cikin adalci wajen siyan sabbin gidaje tare da samar wa kanku da iyalanku mafaka.”
Gwamnan ya jaddada cewa wannan shi ne karo na farko da wani shiri na gwamnati a tsakanin al’umma ba wai kawai magance zaizayar kasa ba ne har ma da biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.
Karin karatu: Gwamnatin Kano ta bukaci al’umma su riƙa kai mata rahoton keta dokokin muhalli a yankunansu
Ya kuma ba da tabbaci ga mazauna yankin na ci gaba da ba da tallafi, tare da yin alƙawarin ƙarin ayyukan da suka shafi ɗan adam a yankin.
A nasa jawabin, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano kuma kodinetan ayyukan ACRESAL na jihar, Dr. Dahir M. Hashim, ya yabawa jagorancin gwamnan wajen amincewa da shirin biyan diyya.
Ya bayyana cewa an biya Naira miliyan 642 ne daga Majalisar Zartarwa ta Jiha kafin a fara aikin kawar da zaizayar kasa.
Dakta Hashim ya bayyana cewa an yi watsi da yawancin gidajen da abin ya shafa sama da shekaru goma, kuma yankin ya zama cibiyar rashin tsaro da aikata laifuka.
Ya ba da labarin yadda yara ke tsallakawa wurin da zaizayar kasa domin zuwa makaranta, inda wani mummunan lamari ya faru a lokacin damina da ya yi sanadin mutuwar dalibai 11.
Babu adadin kuɗi da ya fi ran ɗan adam daraja,” in ji shi. “Wannan aikin ya wuce abubuwan more rayuwa; yana da nufin ceton rayuka da maido da farin ciki.”
Kwamishinan ya yabawa bankin duniya, gwamnatin tarayya, da kuma gwamnatin jihar bisa samar da isassun kudade domin biyan diyya ga mutanen da abin ya shafa.
A nasu bangaren, wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna jin dadinsu ga gwamnatin jihar Kano da kuma shirin da bankin duniya ke tallafawa, ACRESAL, bisa daukar matakin da ya dace.
Fatima Bashir, wadda ta samu N319,755,000, ta ce diyya za ta taimaka mata wajen sake gina rayuwarta. “Na yi godiya sosai, wannan kuɗin zai taimaka mini wajen samun sabon gida ga iyalina.”
Sale Sabo Ibrahim, wanda ya samu N1,118,180,000, ya bayyana mamaki da godiya. “Ba mu taba yarda cewa wannan rana za ta zo ba, gwamnati ta tabbatar da cewa tana saurare kuma tana kulawa.”
Fatima Haruna wadda ta samu Naira miliyan 442,500,000 ta kuma godewa gwamnati kan yadda ta fifita jin dadin al’umma. “Wannan sabon mafari ne a gare mu, Allah ya sakawa gwamna da tawagar ACRESAL”.