Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da sabuwar Majalisar masarautar Kano da aka sake fasaltawa, wadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ke jagoranta tare da sauran sarakuna uku na Gaya da Karaye da Rano a matsayin mambobi.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kaddamarwar ta zama sabon babi a tarihin masarautar Kano, bayan rattaba hannu da Gwamna Yusuf ya yi kan Dokar Majalisar Masarautun Kano ta 2024, wadda ta rushe masarautu biyar da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa.
A wajen bikin da aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnati, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kafa majalisar na da nufin ƙarfafa tasirin masarauta wajen kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban jihar.
Ya kuma jaddada cewa masarauta ginshikin tarihi ce, mai rike al’adu, da tsarin zaman lafiya, da kuma muhimmincin abokantaka da gwamnati.
Gwamnan Abba ya bayyana cewa kafuwar majalisar na nuni da kudirin gwamnati na kare gadon al’adun Kano da inganta kyakkyawan mulki, tare da samar da dandalin da sarakuna za su tattauna su ba da shawarwari kan al’amuran da suka shafi jin dadin al’umma.
Mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bayyana fatancewa majalisar za ta taka rawar gani wajen ci gaban jihar.
Mai ba da shawara kan harkokin sarauta Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya yi bayani kan tarihin masarautar Kano da alaƙarta da Rano da Gaya da Karaye, yana mai cewa Gwamnan ya dawo da tsarin tarihi na hadin kai cikin masarautun sama da shekaru 700.
Sarkin Kano kuma shugaban majalisar Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ce dawo da majalisar ya yi daidai da tushen tarihi, yana yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa manyan abubuwan da ya cimma a jihar, tare da tabbatar da cewa sarakuna za su ba da gudummawa sosai domin cigaban Kano.













































