Gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia, ya yi Allah wadai da kisan wasu ‘yan asalin jihar Kano biyu da wasu ‘yan ta’adda suka yi a mazaunin su da ke yankin Agan na jihar.
SolaceBase ta ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban dabbanci kuma ba za a amince da shi ba, inda ya bayyana cewa dole ne a kamo wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su gaban kuliya cikin gaggawa.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Tersoo Kula ya fitar a Talatar makon nan.
A cewar sanarwar, ya zuwa yanzu, tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta cafke wasu masu laifi mutum biyar a garin Makurdi bisa wannan kisa biyo bayan umarnin da gwamnan ya bayar tun da farko ga kwamishinan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da abun ya shafa na ganin an kama wadanda suka aikata laifin.
‘’Gwamnan ya yi matukar alhinin rasuwar wasu mutane biyu da aka bayyana ‘yan asalin jihar Kano ne da ke gudanar da harkokinsu jihar, amma wasu bata gari suka kai musu mumunan hari tare da kashe su.
Ya ce, “An san mutanen Binuwai da karimci da zaman lafiya, ba za mu iya barin wasu ’yan ta’adda su rika bata mana suna da kuma zubar mana da kima ga ba, dole ne a kama wadannan masu laifin nan ba da jimawa ba kuma a sa su fuskanci fushin doka.
‘’Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga takwaransa na Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa wannann iftila’i na kisan ‘yan asalin Kano mutum biyu.
Da sanyin safiyar yau ne Gwamnonin biyu suka yi magana kan wannan mummunan lamari.
gwamnan , ya kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa za a yi adalci.













































