Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya kori Hajiya Zainab Baban-Takko daga kujerar Kwamishinar harkokin Mata da cigaban yara nan take.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Mukhtar Gidado, ya fitar da safiyar Litinin.
A cewar Gidado, wannan mataki na zuwa ne sakamakon ƙaramin sauyi da gwamnan ya yi a cikin tsarin majalisar zartarwar jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya gode wa kwamishinar bisa gudunmawar da ta bayar ga jihar a lokacin da take rike da mukamin, tare da yi mata fatan alheri a ayyukan ta na gaba.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa wannan sauyin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati wajen inganta tsarin gudanarwar jihar domin tabbatar da cigaba ga al’umma.
NAN













































