Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, da Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi, sun buƙaci Gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin aikin gyaran madatsar ruwa ta Alau.
Gwamnan da Shehun Bornon sun mika bukatar hakan ne a lokacin da Shehun ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan a Fadar Gwamnatin jihar dake Maiduguri, inda suka jaddada muhimmancin aikin domin hana afkuwar makamanciyar ambaliyar da aka samu a baya.
Gwamna Zulum ya nuna damuwarsa kan jinkirin aikin, yana mai cewa akwai buƙatar a ɗauki mataki cikin gaggawa kafin zuwan damina. Inda ya yi gargadin cewa, idan ba a hanzarta ba, jihar na iya fuskantar wata ambaliya mai haɗari kamar ta shekarar 2024.
Gwamnatin Tarayya ta amince da ware Naira biliyan 80 don aikin, wanda aka kaddamar a watan Maris.
Wannan roƙo nasu dai na zuwa bayan da al’ummar garin na Alau da ma mazauna Borno suka fara nuna fargaba ganin damina ta fadi.












































