Gwamna Tambuwal ya yi fatali da sakamakon masalaha tsakanin ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP.

Tambuwal new
Tambuwal new

Gwamnan jihar Sokoto kuma mai fatan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi watsi da sakamakon tsarin maslaha tsakanin yan takara daga yankin Arewa inda yace ba abune mai yiwuwa ba.

Tambuwal ya kuma soki lamirin rahoton da kwamitin sulhu ya fitar karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi, wanda ya sanya ‘yan takarar shugaban kasa biyu, Dakta Bukola Saraki da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin su ne yan takarar PDP biyu daga yankin Arewa a zaben 2023.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Juma’a mai dauke da sa hannun Daraktan Kungiyar wayar da kai da kuma Yakin neman zaben Tambuwal wato TCO, Nicholas Msheliza.

Sanarwar ta ce, dukkan ‘yan takarar shugaban kasa hudu da suka yarda da tsarin maslaha tun da farko sune suka gaza a tsarin, don haka ba za a iya bayyana Bukola Saraki da Bala Mohammed a matsayin Yan takarar da suka dace a yankin Arewa ba.

2 SHARHI

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here