Gwamna Radda ya sauya kwamishinoninsa, ya kuma ƙirƙiri sabuwar ma’aikata

Dikko Radda new 750x430 (1)

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya amince da sake fasalin kwamishinonin majalisar zartarwarsa tare da ƙirƙirar sabuwar ma’aikata mai kula da ci gaban harkokin kiwo.

A cewar mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula-Mohammed, wanda ya fitar da sanarwar a ranar Asabar a Katsina, sauyin ya fara aiki nan take domin ƙara inganta gudanar da ayyukan gwamnati.

Sanarwar ta ce, an mayar da Alhaji Adnan Nahabu daga ma’aikatar ayyuka na musamman zuwa ma’aikatar ilimin gaba da sakandare da koyon sana’o’i, yayin da Farfesa Ahmad Muhammad-Bakori daga ma’aikatar noma da kiwo ya koma jagorantar sabuwar ma’aikatar harkokin kiwo.

Haka kuma, an tura Alhaji Aliyu Lawal-Zakari daga ma’aikatar wasanni zuwa ma’aikatar noma, sannan Hajiya Zainab Musa-Musawa daga ma’aikatar ilimin firamare da sakandare zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman.

An kuma nada Alhaji Yusuf Suleiman-Jibia a matsayin kwamishinan ilimin firamare da sakandare, sai Alhaji Surajo Yazid-Abukur a matsayin kwamishinan matasa da wasanni, yayin da Hajiya Aisha Aminu, tsohuwar darakta janar ta hukumar bunƙasa kasuwanci ta jihar, ta zama kwamishinar harkokin mata.

Hajiya Hadiza Abubakar-Yar’adua an tura ta daga ma’aikatar mata zuwa ofishin mai ba da shawara na musamman kan abinci mai gina jiki da jin daɗin jama’a, yayin da Alhaji Isa Muhammad-Musa ya koma ofishin mai ba da shawara kan al’adun gargajiya.

Gwamna Radda ya bukaci sabbin kwamishinonin da su dage wajen aiwatar da manufofin shirin “Gina Makomarka”, tare da ba da fifiko ga hidima ga jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa sake fasalin zai ƙara haɗin kai, ƙwarewa da saurin aiwatar da shirye-shirye a sassa kamar ilimi, lafiya, noma, matasa, mata da walwalar jama’a.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here