Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da murabus ɗin kwamishinoni bakwai da suka miƙa takardun ajiye aiki.
Solacebase ta ruwaito cewa a daren ranar Asabar ɗin da ta gabata ne gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da mukaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen baɗi da su miƙa takardar yin murabus ɗinsu daga ranar 18 ga Afrilu ko kuma kafin ranar kamar yadda dokar zabe ta 84 (12) wadda aka yi wa gyara a bana ta tanada.
Duk da cewa akwai jita-jita da ke cewa gwamnan ya ƙi amincewa da murabus ɗin shugaban ma’aikatansa Ali Makoda da kwamishinan ilimi, Muhammad Sanusi Saidu Kiru, kwamishinan lafiya Dr. Ibrahim Tsanyawa da kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Nura Muhammad Dankade.
Haka kuma, a kwanan baya gwamnatin Kano ta ƙi amincewa da murabus ɗin shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa KAROTA Baffa Babba Dan’agundi wanda ke nuni da cewa yana son ci gaba da harkokinsa na siyasa.
Wata sanarwa da Babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar yau Talata, ta ce Kwamishinoninsa aka amince da murabus ɗin nasu sun haɗa Dr. Nasir Yusuf Gawuna , Kwamishinan Noma da Albarkatun ƙasa Murtala Sule Garo Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarauta sai Ibrahim Abubakar Karaye kwamishinan al’adu da yawon bude ido.
Sauran sun haɗa da Mahmud Muhammad Santsi kwamishinan gidaje da sufuri da Muntari Ishaq Yakasai kwamishinan ayyuka na musamman da Musa Ilyasu Kwankwaso kwamishinan raya karkara da cigaban al’umma sai kuma Kabiru Ado Lakwaya kwamishinan matasa da wasanni
‘’Gwamnan ya gode musu bisa ga gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar tare da yi musu fatan alheri a al’amuran da suka sanya a gaba, Dangane da haka, an umarci manyan sakatarorin ma’aikatun da abin ya shafa su karɓi ragama ci gaba da ayyuka,” in ji sanarwar.
“Duk da haka, an umurci shugaban ma’aikata da sauran wasu kwamishinonin da su ci gaba da gudanar da ayyukansu a ma’aikatun su.”













































