Gmnwatin Kano ta rufe wani asibiti saboda rashin ƙwarewa

Sealed hospital
Sealed hospital

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata cibiyar lafiya mai zaman kanta sakamakon samun mutum biyu da suka mutu a asibitin cikin watanni shida da suka gabata.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu (PHIMA) na Jihar Kano, Dr. Dakta Usman Tijjani Aliyu ne ya sanar da rufe cibiyar a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce hukumar ta samu rahoto daga wani kwamitin alúmma kan mutuwar majinyata biyu a asibitin, na Green-olives, da ke Sabon titi Tal’udu Gadon kaya a karamar hukumar Gwale.

“Hukumar ta binciki lamarin sosai wanda ya nuna rashin da’a da kuma rashin gudanar da ayyukan da ake yi wa majinyata a cibiyar. Ba a sanya hannu kan fom ɗin ba da izini ba kafin tiyata, marasa lafiya ba su da isasshen shiri kafin tiyata kuma ba a sa ido kan marasa lafiya a lokacin tiyata, ” in ji sanarwar.

A cewar sanarwar, ”Likitan fida yana aiki ne a matsayin ma’aikaciyar jinya, ma’aikacin jinya kuma na aikin mataimakin likitan fida shi ma, don haka shi kadai ke yin ayyuka hudu a lokacin tiyata, kuma wannan rashin da’a ne ga dukkan alamu.”

”Saboda haka, za a yi maganin mai laifin bisa ka’idojin hukumar.” Inji sanarwar

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da hada kai da mutanen jihar Kano da sauran kungiyoyin farar hula domin yakar bara-gurbi da rashin kula da marasa lafiya a asibitoci masu zaman kansu da ke fadin jihar, inda kuma ta yi kira ga jama’a da su kai rahoto a duk inda suke a Kano. domin daukar matakin gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here