Masu rajin kare haƙƙin bil’adama na jimamin rasuwar wani jagoran yawon buɗe ido ɗan kasar Zimbabwe da wata giwa ta tattake har ya mutu a wani gandun daji na Gondwana da ke Afirka ta Kudu.
David Kandela, mai shekaru 36, yana jagorantar gungun masu yawon bude ido ne a yammacin Lahadin da ta gabata, lokacin da bala’in ya faru, in ji masu kula da gandun dajin a cikin wata sanarwa da kafofin yada labarai na kasar suka rawaito.
Karin labari: Laberiya ta kori wasu jami’an tashar jiragen ruwa kan cin hanci da rashawa
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne yayin da tawagar giwaye ke wucewa ta sansanin Eco na Gondwana.
Sanarwar ta kara da cewa, “Tawagar giwayen sun kusa wucewa ta sansanin lokacin da Kandela ya ci karo da giwa ta karshe da ta rage kafin afkuwar lamarin.”
Karin labari: Gwamnan Kano ya karbi bakuncin tawagar bankin Duniya
Abokan jagororin yawon buɗe ido da masu gudanar da yawon shakatawa sun bayyana Kandela a matsayin ƙwararre mai jagora wanda ke da sha’awar aikinsa.
Sun ce ba kasafai irin wannan lamarin ke faruwa ba.
Giwaye dai sun kasance babbar abun sha’awar gani a lokacin yawon bude ido a kudancin Afirka.