Gidauniyar Sen. Barau ta fitar da sunan waɗanda suka ci gajiyar tallafin Karatu

Barau JIBRIN SABO 600x430

Halima Lukman

Gidauniyar Barau I. Jibrin BIJF wadda Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Dakta Barau I. Jibrin ya kafa, ta fitar da jerin rukunin farko na tallafin karatun Digiri na biyu a ƙasashen waje na bana a fannin fasahar ƙere-ƙere da fasahar tsaro da kuma karatu a fannin fashar da ke aiki da ɗabi’ar Ɗan-Adam.

Sanata Barau, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar ECOWAS na farko, ya kafa gidauniyar ne domin samar da ayyukan jin kai, ilimi da karfafawa a kasar.

Wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar a ranar Alhamis, ta ce gidauniyar ta samu gurbin karatu ga daliban da suka cancanta daga gundumomin sanatoci uku na jihar Kano (Kano ta tsakiya, Kano ta Arewa da kuma Kano ta Kudu). don bin Shirye-shiryen Digiri na biyu a ƙasashen waje.

Sanarwar ta ce an dauki shirin bayar da tallafin ne a matsayin wani bangare na kokarin mataimakin shugaban majalisar dattijai na inganta ilimi da kuma karfafa ci gaban fasahar kasar.

“Shirin bayar da tallafin karatu ya takaita ne ga bayanan sirri, fasahar mutum-mutumi, tsaro ta yanar gizo da kuma kimiyyar shari’a daidai da burin mataimakin shugaban majalisar dattijai na bayar da gudummawar wajen magance karancin kwararru a wadannan fannoni na musamman,” in ji sanarwar.

Ya kuma kara da cewa za a raba wa wadanda suka ci gajiyar takardar ne a ranar Litinin 9 ga watan Satumba, 2024 a dakin taro na Amani Event Centre, jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here