Gbajabiamila ya sauka daga kujerar ɗan majalisa

download 4 1
download 4 1

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya sauka daga kujerarsa ta ɗan majalisar wakilan Najeriya, domin fara aiki a sabon muƙaminsa na shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.

Sabon kakakin majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanto wasiƙar murabus ɗin nasa a zauren majalisar ranar Laraba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa mista Gbajabiamila a matsayin sabon shugaban ma’aikata na fadarsa.

Mista Femi dai ya samu nasara a zaɓen kujerar ɗan majalisar wakilan ƙasar mai wakiltar mazaɓar Surulere ta ɗaya a jihar Legas

An dai yi ta nuna damuwa kan yadda ɗan majalisar zai tafiyar da muƙaman biyu, bayan da ya ƙarbi rantsuwa tare da sauran ‘yan majalisar sabuwar majalisa ta 10 ranar Talata, har ma ya jefa ƙuri’arsa a zaɓen shugabannin majalisar.

A yanzu hukumar zaɓen ƙasar za ta shirya zaɓen cike-giɓi na ɗan majalisar wakilan mazaɓar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here