Gamayyar Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya (ASCSN) ta bayyana godiya ga hukumomin tsaro bisa kubutar da daraktoci huɗu na Ma’aikatar Tsaro da aka sace.
Shugaban ƙungiyar, Malam Shehu Mohammed, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar tare da sakatare-janar na ƙungiyar, Malam Joshua Apebo, inda ya yi bayanin cewa an cimma nasarar sakin mutanen ne a ranar Juma’a a Abuja.
Ƙungiyar ta ce an sace daraktocin ne a ranar 10 ga Nuwamba yayin da suke tafiya a kan babban titin Kabba zuwa Lokoja zuwa Abuja domin jarabawar karin girma.
Ta ce mutune huɗu daga cikin mutane shida da aka sace sun samu ‘yanci, kuma ana duba lafiyarsu a cibiyoyin lafiya.
Haka kuma ƙungiyar ta bayyana sunayen mutanen da aka ceci da suka haɗar da: Hajiya Helen Ezeakor, Hajiya Ladoye C. A., Hajiya Ngozi Ibeziakor da Hajiya Essien Catherine O., yayin da Hajiya Emeribe C. A. da Hajiya Onwuzurike J. A. har yanzu ba a same su ba.
Ƙungiyar ta roƙi Ma’aikatar Tsaro da hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi domin ceto sauran jami’an biyu ba tare da wani lahani ba, tare da sake jaddada bukatar warware tsarin gudanar da jarabawa da tantancewa a wurare mabambanta domin rage haɗarin tafiye-tafiye ga ma’aikata.
Ta kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da yake yi na rage matsalar rashin tsaro da tabbatar da tsaro ga matafiya a ƙasar.
NAN













































