Shugaban Rundunar Sojojin Kasa Laftanar Janar Waidi Shaibu ya umurci dakarun Operation FANSAN YANMA da su ƙara tsananta kokari domin kubutar da daliban da aka sace daga Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata a Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi.
Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran dakarun rundunar Operation FANSAN YANMA, Kyaftin David Adewusi, ya fitar a ranar Talata ta bayyana cewa Janar Shaibu ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin ziyarar duba aikin tsaro a Jihar Kebbi.
Yayin jawabi ga manyan kwamandoji da dakarun rundunar, Janar Shaibu ya umurce su da su gudanar da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri tare da bin sawun mahara ba kakkautawa, dare da rana domin ceto daliban.
Ya bayyana cewa wajibi ne a nemo daliban, kuma su yi aiki cikin gaggawa da ƙwarewa bisa bayanan sirri domin tabbatar da nasara.
Shugaban sojojin ya gana da kungiyar masu sintiri da mafarauta na yankin, inda ya yi bayanin cewa suna da muhimmiyar rawa wajen taimakawa aikin.
Karin labari: Kebbi: Jam’iyyun PDP da ADC sun yi Allah wadai da sace ɗalibai mata 25 da kashe mataimakin shugaban makarantar
Ya bukace su da su yi amfani da sanin da suke da shi kan yankin tare da dakaru domin gano inda miyagu suke da kuma kawar da su.
Janar Shaibu ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Danko Alhaji Abubakar Ibrahim Allaje da kuma shugabar makarantar GGCSS Maga Hajiya Rabi Musa Magaji, inda ya tabbatar musu da cewa sojoji za su yi iya bakin kokarinsu domin kubutar da daliban ba tare da wata illa ba.
Haka kuma Janar Shaibu ya bukaci dakaru su kasance masu juriya da ƙwarewa, tare da yin aiki cikin ƙa’idojin runduna, da kasancewa masu saurin daukar mataki, ladabi, da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Kebbi da yankunan da ke kewaye.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigar sun sace dalibai 25 daga makarantar yan mata da ke Maga a Jihar Kebbi, bayan sun shiga makarantar da daddare a ranar Lahadi, inda suka yi harbi suka kashe mataimakin shugaban makarantar Malam Hassan Makuku kafin su yi awon gaba da dalibai mata da dama.
Shaidu sun bayyana cewa barayin sun yi harin ba tare da wata tsangwama ba, lamarin da ya haifar da firgita da tashin hankali a yankin.
Makuku ya rasa ransa ne yayin kokarin kare daliban lokacin harin.













































