Fitaccen tauraron fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu a birnin Mumbai yana da shekara 89 lamarin da ya girgiza masana’antar nishadi.
Fira Ministan Indiya Narendra Modi ya bayyana rasuwar a matsayin babban gibi ga masana’antar, inda ya yi nuni da cewa mutuwarsa ta kawo ƙarshen wani zamani da ya yi fice a tarihi.
Dharmendra ya shahara wajen shaƙuwa da masoyansa duk da matsayinsa a masana’antar Bollywood, kuma an fi tunawa da shi a matsayin Veeru a fim ɗin Sholay na shekarar 1975.
Ya fito a fina-finai sama da dari uku a cikin dogon aikin da ya yi, tare da samun karɓuwa a fannonin soyayya, ban dariya, faɗa da kuma jarumta.
Haka kuma dangantakar sa da fitacciyar jaruma Hema Malini ta zama ɗaya daga cikin labaran soyayya da suka yi fice a masarautar Bollywood.
An haife shi a matsayin Dharam Singh Deol a garin Nasrali da ke jihar Punjab, inda ya tashi a cikin iyali mai matsakaicin hali.
Ya fara sha’awar fim tun yana ƙarami duk da ƙin amincewar iyayensa, kuma bayan ya lashe gasar baiwa ta ƙasa baki ɗaya da jaridar Filmfare ta shirya, ya koma Bombay domin cika burinsa na zama ɗan wasa.
Wannan ya fara nuna masa hanya zuwa shahara tun bayan fitowarsa a fim ɗin da ya fara bayyana a ciki a shekarar 1960.
Dharmendra ya samu karin farin jini ne bayan fitowarsa a fim ɗin Bandini, sannan ya ci gaba da taka rawa a manyan fina-finai da suka haɗa da Phool Aur Patthar da Mera Gaon Mera Desh, inda ya rika yin yawancin abubuwan faɗa da kansa.
Dangantakarsa ta fim da Hema Malini ta ƙara masa suna, kuma ta rikide zuwa auren su a shekarar 1980 duk da cece-kuce da ya biyo baya.
A wajen harkar fim, Dharmendra ya shiga siyasa na ɗan lokaci inda ya wakilci yankin Bikaner a majalisar dokoki ta jihar Rajasthan daga shekarar 2005 zuwa 2009, kodayake daga baya ya ce harkar siyasa ba ta dace da shi ba.
Ya ci gaba da fitowa a fina-finai tare da ‘ya’yansa Sunny da Bobby Deol, kuma ya kasance yana mu’amala da masoya ta kafofin sada zumunta.
Aikinsa a fim ɗin Sholay ya kasance abin da ya fi daukar hankali, inda ya bayyana jarumin Veeru a matsayin rawar da ya fi so a rayuwarsa.
Wannan rawar ta zama abin koyi ga masoya da masana, kuma ta ƙarfafa matsayin sa a matsayin daya daga cikin fitattun jaruman da suka yi tasiri a masana’antar Bollywood ta Indiya.
Dukkan wannan ya sa ya samu lambar yabo ta Filmfare ta girmamawa gaba ɗaya a shekarar 1997 tare da girmamawar Padma Bhushan a shekarar 2012.
Bayan rasuwarsa, masana’antar Bollywood da masoya daga sassa daban-daban na duniya sun rika bayyana jimaminsu, suna mai cewa Dharmendra ya bar babbar gada ta bajinta, ƙwarewa da soyayya da ba za a manta da ita ba.
Ya kasance tauraro wanda ya sanya annashuwa, ƙarfi da karsashi a fina-finai, yana barin abin tunawa da zai ci gaba da rayuwa a zukatan al’umma a ko’ina.













































