Faransa ta gargaɗi ‘yan kasarta kan tafiya arewacin Mozambique

Faransa, 'yan kasa, gargadi,
Ofishin jakadancin Faransa da ke Mozambik ya gargadi 'yan kasarsa kan yin tafiya zuwa lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar saboda rashin tsaro a wannan...

Ofishin jakadancin Faransa da ke Mozambik ya gargadi ‘yan kasarsa kan yin tafiya zuwa lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar saboda rashin tsaro a wannan yanki na kasar.

“Muna ba da shawara mai karfi game da tafiya zuwa garuruwan Mocimboa da Praia da Pemba da Palma, da hanyoyin da suka hada su saboda barazanar ta’addanci da sace-sacen jama’a,” in ji wata sanarwa da aka raba a shafin intanet na ofishin jakadancin.

Karanta wannan: Najeriya na kan tsini – Sultan Sa’ad

Gargadin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka buɗe wuta a kan mazauna garin tare da ƙona majami’u huɗu da wata makarantar Kirista a wani hari da suka kai a gundumar Chiure.

Cabo Delgado ya sami karuwar ayyukan tsageru a cikin watan da ya gabata, yayin da kafofin yaɗa labarai na cikin gida suka ba da rahoton hare-hare sama da 12 a cikin makonni biyu na farkon shekarar 2024.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here