Fadar shugaban ƙasa ta yabawa Kwankwaso bisa kishin ƙasa da ya nuna wajen sukar Triumph da barazanar yaƙi da ya yiwa Najeriya

RMK RMK 554x430

Fadar shugaban ƙasa ta yaba wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa nuna kishin ƙasa da ya yi wajen sukar maganganun shugaban ƙasar Amurka Donald Trump da ke barazanar ƙaddamar da yaki a kan Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya bayyana matsayin Kwankwaso a matsayin abin yabawa, yana mai kira ga ‘yan adawa su manta da siyasa su tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin Najeriya daga abin da ya kira “ƙalubale daga waje.”

Ya ce lokaci ne da ya dace duka shugabannin siyasa su haɗa kai don kare martabar ƙasar, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyu ba.

Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa kalaman Trump na iya tayar da ƙiyayyar addini da ƙara dagula matsalar tsaro a Najeriya.

Karanta: Fadar shugaban ƙasa ta musanata ziyarar Tinubu zuwa Amurka

Tsohon gwamnan ya bayyana a shafinsa na X cewa matakin Trump na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kira “ƙasashen da ake da damuwa da su” saboda zargin kisan gilla ga Kiristoci, ba gaskiya ba ne, domin matsalolin tsaro a ƙasar ba su da alaƙa da addini ko kabila.

Kwankwaso ya bukaci gwamnatin Amurka ta taimaka wa Najeriya da fasaha da bayanan sirri maimakon barazana, tare da shawartar gwamnatin tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen hulɗar diflomasiyya da tura jakadu a ƙasashen da ke da muhimmanci ga alakar ƙasa.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su tsaya tare cikin haɗin kai da kishin ƙasa don fuskantar ƙalubalen da ke gaban su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here