Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya na da ikon zaɓar abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ne kawai bayan ya amince da takarar jam’iyyar a lokacin babban taronta na shekarar 2026 da ke tafe cewar Bayo Onanuga, mashawarci na musamman ga shugaban kan harkokin yaɗa labarai da dabaru.
Onanuga, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust.
Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa fadar shugaban ƙasa ta yi shiru yayin da ake ci gaba da samun cece-kuce kan batun cire mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, daga cikin rade-radin amincewa da Tinubu, Onanuga ya yi watsi da shawarar da aka yaɗa ta cewa shirun ya yi dai-dai da amincewar cire mataimakin shugaban kasa.
“Lokacin da na karanta labarin sai na yi watsi da shi a matsayin ba wani batu ne na gaskiya ba, a tsarin shugaban kasa, dan takara ya fara fitowa sannan ya zaɓi wanda zai yi takarar mataimaki, abin da ya faru kenan a karkashin Buhari, shi ne aka fara tsayar da shi, daga baya kuma ya zabi abokin takararsa, ba za ku yi duka biyu lokaci daya ba.
“Da zarar INEC ta fitar da jadawalin, babban taron jam’iyyar zai yi, kuma idan aka sake zaɓen shugaban kasa, zai zabi abokin takararsa,” inji shi.
Onanuga ya kuma yi watsi da ikirarin da Tinubu ya yi a matsayin gwamnan jihar Lagos, inda ya sauya mataimaka har sau biyu ya na nuna shirin ajiye Shettima kafin 2027.













































