Kwamitin raba kuɗaɗen asusun tarayya (FAAC) ya bayyana cewa ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.22 tsakanin matakan gwamnati uku a watan Agusta.
Wannan adadin ya fito daga cikin jimillar kudaden shiga na Naira tiriliyan 3.63.
A wata sanarwa daga ma’aikatar kuɗi ranar Laraba, wanda taron FAAC na watan Satumba a Abuja ƙarƙashin jagorancin ministan kuɗi, Wale Edun, ya tabbatar da rabon kuɗaɗen.
An bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu N810.05 biliyan, jihohi N709.83 biliyan, yayin da kananan hukumomi suka karɓi N522.23 biliyan.
Haka kuma jihohin da ke samar da mai sun samu N183.01 biliyan a matsayin kaso na 13 bisa ɗari.
Sanarwar ta ce an ware N124.84 biliyan a matsayin kuɗin taro, sannan Naira tiriliyan 1.28 aka tura zuwa asusun sauye-sauye, tallafi da mayar da kuɗi.
FAAC ta kuma bayyana cewa kudaden da aka samu daga harajin ƙarin kayayyaki (VAT) a watan Agusta sun kai N722.61 biliyan, abin da ya fi na watan da ya gabata da N34.67 biliyan.
Daga ciki, an ware N28.9 biliyan a matsayin kuɗin taro, da N20.8 biliyan ga tallafi da mayar da kuɗi, yayin da aka raba N672.90 biliyan ga gwamnati uku.
Haka kuma, kudaden harajin doka da aka samu sun sauka zuwa Naira tiriliyan 2.83 idan aka kwatanta da N3.07 tiriliyan da aka samu a watan da ya gabata.
Daga ciki, gwamnatin tarayya ta samu N684.46 biliyan, jihohi N347.16 biliyan, kananan hukumomi N267.65 biliyan, yayin da jihohin mai suka samu N179.31 biliyan a matsayin kaso na 13 bisa ɗari.
FAAC ta ƙara da cewa daga kuɗin harajin ma’amalar kuɗi ta lantarki (EMTL) na N33.68 biliyan, gwamnatin tarayya ta samu N4.85 biliyan, jihohi N16.16 biliyan, kananan hukumomi N11.31 biliyan, sannan N1.34 biliyan aka ware shi a matsayin kuɗin taro.
Haka kuma, N41.28 biliyan daga bambancin canjin kuɗi an raba shi ga gwamnati uku da kuma jihohin mai.
Kwamitin ya bayyana cewa kudaden harajin mai da iskar gas, VAT da CET sun ƙaru, yayin da harajin ribar man fetur (PPT), harajin shigo da kaya, EMTL, harajin kamfanoni (CIT) da harajin kaya suka ragu. Jimillar kuɗaɗen da aka raba a watan Agusta ta fito daga harajin doka na N1.47 tiriliyan, VAT na N672.90 biliyan, EMTL na N32.33 biliyan da kuma bambancin canjin kuɗi na N41.28 biliyan.
A jawabinsa, Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya yaba wa mambobin FAAC bisa himma wajen tabbatar da rabon kuɗaɗe ga dukkan matakan gwamnati.
Ya ce sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta aiwatar na haifar da sakamako mai kyau, tare da kira da a gudanar da harkokin kuɗi cikin adalci domin amfanin ’yan ƙasa.













































