Kwamitin rabon arziki na tarayya (FAAC) ya raba kudaden shiga da yawan su ya kai Naira tiriliyan 1.703 a tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi na watan Janairu.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin Akanta-Janar na tarayya Bawa Mokwa ne ya sanar da hakan ga manema labarai a karshen taron kwamitin ranar Alhamis a Abuja.
A cewar sanarwar, jimillar kudaden shigar da aka samu na Naira tiriliyan 1.703 ya kunshi kudaden shiga na doka na Naira biliyan 749.727 da kuma kudaden harajin kayayyaki (VAT) na Naira biliyan 718.781.
Kudaden sun ƙunshi kudaden shiga da aka tattara daga harajin kiran waya da yawansu ya kai Naira biliyan 20.548 da kuma wadanda aka ƙara na Naira biliyan 214.
Ya ce an samu jimillar kudaden shiga na Naira tiriliyan 2.641 a cikin watan Janairu, sai kuma jimillar kudaden shiga da aka kayyade na Naira tiriliyan 1.848 na watan Janairu.
“Wannan ya zarce Naira tiriliyan 1.226 da aka samu a watan Disambar 2024 da Naira biliyan 622.125″.
Sanarwar ta ce daga jimillar kudaden shiga na Naira Tiriliyan 1.703, Gwamnatin tarayya ta samu Naira Biliyan 552.591 sannan gwamnatocin Jihohin kasar nan sun samu Naira Biliyan 590.614, sai ƙananan hukumomi da suka samu Naira biliyan 434.567 kuma an raba jimillar Naira biliyan 125.284 (kashi 13 na kudaden shiga na ma’adinai) ga jihohin da suka amfana a matsayin kudaden shiga.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, daga kudaden harajin VAT na Naira biliyan 718.781, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 107.817, gwamnatocin jihohi kuma sun karbi Naira biliyan 359.391, sai kuma kananan hukumomi da suka samu Naira biliyan 251.573.
Ya ce, Jimillar Naira Biliyan 3.082 ne gwamnatin tarayya ta karbo daga Naira Biliyan 20.548 na EMTL, inda gwamnatocin Jihohin kasar suka samu Naira Biliyan 7.192, sai kuma gwamnatin tarayya ta samu Naira Biliyan 10.274. (NAN)