EFCC ta kwace Fasfo ɗin Malami, ta nemi asusun sa don binciken Dala Miliyan 490 na kuɗin Abacha

Abubakar malami san

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kwace fasfo ɗin ƙasa da ƙasa na tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Alhaji Abubakar Malami SAN, yayin da take bincike kan inda kuɗin Abacha na Dala Miliyan 490 suka shiga ta hanyar yarjejeniyar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MLAT).

Hukumar ta hana Malami fita daga ƙasar nan na tsawon wata guda saboda sharadin da aka gindaya a lokacin da aka sallame shi da ƙarfe ɗaya na safiyar asabar wanda ya wajabta ya rinka kai rahoto kullum a hedkwatar EFCC domin ci gaba da tattaunawa kan bincike.

Ya bayyana cewa zarge-zargen da ake yi masa ƙirƙira ne kuma ya yi nuni da cewa gaskiya na kan bayyana.

A bayanan da hukumar EFCC ke da su, akwai abubuwa da dama da ake buƙatar Malami ya fayyace a wannan wata guda, ciki har da cikakken bayanin inda kuɗin Abacha na Dala Miliyan 490 suka tafi.

Hukumar ta ce ba ta zarge shi da laifin satar kuɗi ba amma ya zama wajibi ya bayyana yadda kuɗin suka kasance.

Karanta: An saki tsohon ministan Shari’a Malami bayan amsa tambayoyi daga EFCC

Saboda yawan takardun da ake bukatar ya duba da kuma ganawa da jami’an bincike, hukumar EFCC ta kwace fasfo ɗinsa domin tabbatar da cikakken halartar binciken.

Daya daga cikin sharuddan belinsa shi ne ya rinka gabatar da kansa kullum a hedkwatar hukumar tare da hana shi fita ƙasar nan sai da izinin EFCC ko kotu.

Malami ya bayyana cewa zargin da ake yi masa an tsara shi ne domin bata suna, kuma ya ce gaskiya za ta ci gaba da fitowa yayin da ake sake tattaunawa da shi a hukumar EFCC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here