EFCC ba ta taɓa gayyata ta ba – Jonathan

1687005470112
1687005470112

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya musanta iƙirarin mawaƙin nan Femi Kuti ya yi a kansa, wanda ya ce Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arziƙin ƙasa ta’annati ta gayyace shi kan zargin sha’anin kuɗi bayan wa’adinsa ya ƙare a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa.

A baya-bayan nan mawaƙin ya ce tsohon shugaban Najeriya ya taɓa zuwa EFCC a matsayin wanda aka yi wa tambayoyi ko gudanar da bincike a kan shi, sai dai wata sanarwa da tsohon shugaban ya fitar ta musanta hakan.

A ranar Juma’a ne Wealth Dickson Ominabo wanda jami’in yaɗa labarai ne a ofishin tsohon shugaban ƙasar ya fitar da sanarwar da ta ƙaryata wannan iƙirari.

Inda ya ce ya yi amfani da wasu bayanai da wasu suka riƙa yaɗa wa a baya kan shugaban domin su ɓata masa sunan, har suka riƙa cewa sai da ya je EFCC domin amsa tambayoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here