ECOWAS ta naɗa Osinbajo a matsayin jagoran sa ido kan zaben ƙasar Côte d’Ivoire

Yemi Osinbajo

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta nada tsohon mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo domin jagorantar tawagar sa ido kan zaɓen shugaban ƙasa a ƙasar Côte d’Ivoire.

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Côte d’Ivoire a ranar 25 ga Oktoba, inda kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa za ta tura tawagarta daga ranar 19 zuwa 29 ga watan, bisa tanadin ƙarin yarjejeniyarta kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki.

A matsayinsa na shugaban tawagar, Osinbajo zai jagoranci ƙungiyar ƙwararrun ‘yan Afirka daga ƙasashen yamma don tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a Côte d’Ivoire tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana, gaskiya da lumana ta hanyar dimokuraɗiyya.

Kungiyar ECOWAS ta ce za ta yi aiki tare da sauran ƙungiyoyin masu lura da zaɓe na cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin tantance yadda zaɓen zai gudana da kuma ƙarfafa amincewa da tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Haka kuma, kungiyar ta bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewarta wajen tallafa wa zaman lafiya, kwanciyar hankali da gudanar da sahihin zaɓe a yankin yammacin Afirka.

Ana sa ran wannan zaɓe na ranar 25 ga Oktoba zai kasance mai matuƙar tasiri ga tsarin mulkin dimokuraɗiyya na Côte d’Ivoire, kasancewar shugaban ƙasar, Alassane Ouattara mai shekaru 83, na neman wa’adi na huɗu duk da alkawarin da ya yi a baya na sauka daga mulki bayan kare wa’adinsa na yanzu.

Wannan mataki na shugaban ƙasar ya tayar da ƙura a harkokin siyasa tare da haifar da muhawara kan iyakokin wa’adin mulki da tsarin sauyin mulki na dimokuraɗiyya a ƙasar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here