Hukumar kula da masu yiwa ƙasa hiima (NYSC) ta ƙara wa’adin yin rajista na masu shirin shiga hidimar ƙasa na shekara ta 2025 rukuni na C da awanni 48, inda sabon wa’adin zai kare da tsakar dare ranar Talata, 11 ga Nuwamba, 2025.
Karin wannan lokaci ya biyo bayan matsalar sadarwa da ta hana wasu masu shirin shiga hidimar yin rajista cikin sauƙi a tsarin da ake gudanarwa ta hanyar shafin internet.
Hukumar NYSC ta bayyana cewa tana matuƙar nadamar wannan cikas, tare da tabbatar wa matasan da ake yiwa rajista cewa ana yin aiki dare da rana domin gyara matsalar cikin gaggawa.
Hukumar ta ce wannan matsala ta sa wasu daga cikin masu shirin shiga hidimar suna shan wahala wajen kammala rajistarsu saboda jinkirin da tsarin ke yi.
A cewar daraktar sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta hukumar, Caroline Embu, wannan ƙarin lokaci an yi shi ne domin bai wa matasan damar kammala rajistar su yadda ya dace, yayin da ta gode musu bisa haƙuri da fahimtar da suka nuna.
Hukumar ta bayyana cewa rajistar ta fara ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2025, kuma an tsara za ta kare ranar 9 ga Nuwamba, amma saboda wannan matsalar an tsawaita ta zuwa 11 ga watan don bai wa kowa damar kammalawa.
Haka kuma wasu daga cikin matasan da abin ya shafa sun nuna damuwa da takaici kan yadda tsarin rajistar ke wahalar da su, inda suka bukaci hukumar NYSC ta gyara tsarin domin a samu sauƙin rajista mai inganci.













































