DSS ta gurfanar da wani ɗan gwagwarmaya kan zargin karɓar kuɗi da kuma tsoratarwa a Kaduna

Abubakar Muhammad popularly known as Sultan 750x430

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) a ranar Litinin ta gurfanar da wani matashin dan gwagwarmaya a dandalin sada zumunta, Abubakar Muhammad da ake kira Sultan, a gaban kotun majistire da ke Rigasa a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, bisa zargin karbar kuɗaɗe da kuma barazanar aikata laifi.

An gurfanar da shi a gaban Babban Majistare Muhammad Musa bisa tuhumar laifuka guda biyu da suka shafi garkuwa da kuɗi da kuma yin barazana ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na ƙarya, wanda ya saba da dokar laifuka ta jihar Kaduna ta shekarar 2017.

Lauyan DSS ya bayyana cewa karar ta samo asali ne daga wata mata mai suna Hafsat Yusuf Paki, wacce ta kai ƙorafi kan cewa Sultan ya yi amfani da asusun sada zumunta na bogi wajen barazanar tona mata hotuna na batsa muddin ba ta biya shi ba, ta hanyar kudin cryptocurrency da kuma POS.

Mai gabatar da ƙara ya ƙara da cewa, an kuma yi barazanar garkuwa da ita, duk da cewa bincike bai tabbatar da hakan ba, amma akwai hujjojin farko da suka nuna aikata laifin garkuwa da kuɗi da barazana, shi ya sa aka gurfanar da shi.

Sultan ya musanta laifukan, inda DSS ta nemi a tura shi gidan gyaran hali, amma kotu ta ba shi beli kan naira miliyan ɗaya tare da samun mutane biyu masu ɗaukar nauyi da suka kasance ma’aikatan gwamnati a Kaduna wadanda ba su yi ƙasa da matakin aiki na 16, tare da shaidar hotuna da kuma asusun banki da ke da aƙalla naira miliyan ɗaya.

Kotun ta ce ba a buƙatar a ajiye kuɗin a yanzu, amma za a kwace su idan ya tsallake beli.

An dage shari’ar zuwa ranar 6 ga Oktoba, 2025 don ci gaba da sauraron ƙarar.

DSS ta ce ta kama Sultan ne a Rigachikun a ranar 27 ga Satumba, inda ta gano asusun sada zumuntar da ya yi amfani da su wajen aikata laifin, tare da bin sawun mu’amalolin kuɗi da bayanan dijital.

Hukumar ta ƙara da cewa Sultan ya yi amfani da sunayen bogi a shafukan X (tsohon Twitter) da Instagram wajen yin barazana da kuma neman kuɗi, kuma ta jaddada cewa kama shi ba ta da nasaba da siyasa, illa dai zargin laifukan sadarwa.

DSS ta ce wadda ta kai ƙarar ta ji tsoron rayuwarta da ta iyalinta, shi ya sa ta kai rahoto, lamarin da ya kai ga kama wanda ake tuhuma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here