Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin dan Adam da daidaito a harkokin tattalin arziki (SERAP) ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, da hukumomin da suke yaki da cin hanci da rashawa da su gaggauta binciken zargin sama da Naira biliyan 26 na al’umma, da suka bace, ko kuma aka karkatar da su daga asusun Blbunkasa fasahar harkokin Man Fetur (PTDF) da ma’aikatar albarkatun man Fetur ta tarayya ta yi a shekarar 2021.
An tattara waɗannan bayanai a cikin rahoton da aka tantance na shekarar 2021 wanda Ofishin Babban Odita na tarayya ya buga ranar Laraba 13 ga Nuwambar 2024.
SERAP ta ce, “Duk wanda ake zargi da hannu a cikin lamarin to dole ne ya fuskanci hukunci kamar yadda ya dace, idan akwai isassun shaidun da za a iya amincewa da su, kuma duk wasu kudaden jama’a da suka bace ya kamata a kwato su gaba daya kuma a mika su cikin baitul malin gwamnati.”
SERAP ta bukaci da a yi amfani da duk wani kudaden da aka kwato domin samar da gibin kasafin kudin 2025 da kuma sassauta durkushewar tattalin arziki da bashin da ake bin Najeriya.
A cikin wasikar mai dauke da kwanan wata 1 ga Fabrairu 2025 dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Akwai hakkin jama’a wajen tabbatar da adalci da kuma bin diddigin wadannan zarge-zarge. Yaki da cin hanci da rashawa a fannin man fetur zai taimaka sosai wajen magance gibin kasafin kudi da matsalolin basussuka.